An kashe mutane 19 a harin kunar bakin wake a Afganistan

Mutane 19 ne suka mutu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a jihar Nangarhar da ke gabashin Afganistan.

An kashe mutane 19 a harin kunar bakin wake a Afganistan

Mutane 19 ne suka mutu sakamakon harin kunar bakin wake da aka kai a jihar Nangarhar da ke gabashin Afganistan.

Kakakin Fadar gwamnann Nangarhar Ataullah Hogyani ya ce, wani mutum dauke da bama-bamai a jikinsa ne ya shiga tsakanin masu zanga-zangar adawa da gwamnati a yankin Dehkai tare da tayar da su.

Hogyani ya kara da cewar mutane 19 aka kashe tare da jikata wasu 57 a harin.

Mutanen sun gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati saboda zargin da suka yi wa masu tsaron kauyen na zaluntar jama'a.

Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.

 Labarai masu alaka