An kashe mayakan Houthi da dama a Yaman

An kashe mayakan Houthi da dama a kasar Yaman sakamakon hare-haren da dakarun kawancen kasashe da Saudiyya ke jagoranci da na gwamnati suka kai a garin Hudayd da ke yammacin Kasar.

Bangaren mayakan Houthi başce komai ba game da wannan batu.

A lokacin da ake ci gaba da samun arangama tsakanin mayakan Houthi da na gwamnati a Hudayd, dakarun Yaman sun kara kwace wasu yankuana.

Tsawon lokaci ana rikicin siyasa a Yaman inda a watan Satumban 2014 mayakan Houthi suka kori gwamnati tare da kwace San'a babban birnin kasar da wasu yankuna.

Kawanden Kasashen Larabawa da Saudiyya ke wa jagoranci kuma sun fara kai wa Houthi hare-hare ta sama tun shekarar 2015 inda suke taimakawa gwamnatin da ta mayar da helkwatarta birnin Aden.

Tag: Hari , Hudayd , Yaman

Labarai masu alaka