Turkiyya ta daura damarar dakatar da hare-haren da ake kaiwa Idlib

Ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya bayyana cewar Turkiyya ta daura damarar dakatar da hare-haren kin Karin da ake kaiwa ta sama a yankin Idlib.

A yayinda yake jawabi a wani taron yankin Mediterranean a Antalya ya ja kunne da cewar kai hari a yankin zai jefa fararen hula cikin mawuyacin hali a yankin da keda mazauna miliyan uku da rabi.

Cavusoglu ya yi fatan warware rikicin yankin Idlib cikin ruwan sanyi, inda ya kara da cewa Turkiyya na kara maida himma tare da haddin gwiwar Rasha da Iran domin kawo karshen matsalolin yankin.

AALabarai masu alaka