Akwai yiwuwar wata mummunar guguwa ta kunna kai Amurka

Hukumomi a Amurka sun yi gargadi game da yiwuwar girmamar guguwar "Florence" wadda a mako mai zuwa ake sa ran za ta tunkari jihohin gabashin kasar.

Kwararrun kula da yanayi sun ce, a yanzu guguwar na a yanki mai nisan kilomita dubu 2,414 a tekun Oceanic kuma tana neman sauya wa ta koma mummunanr guguwa mai daraja ta 1.

Kwararrun suun ce, a ranar Alhamis mai zuwa guguwar za ta dangana da gabar tekun gabashin Amurka.

Sakamakon guguwar "Florence" an sanar da dokar ta baci a jihohin Virginia, North Carolina da South Carolina da ke gabashin Amurka.

An sanar da cewar akwai yiwuwar guguwar ta dangana ga jihar Georgia.Labarai masu alaka