Girgizar kasa mai ban tsoro ta sake afkuwa a Indonesiya

Girgizar kasa mai karfin awo 6.9 ta sake afkuwa a tsibirin Lombok na Kasar Indonesiya.

Girgizar kasa mai ban tsoro ta sake afkuwa a Indonesiya

Girgizar kasa mai karfin awo 6.9 ta sake afkuwa a tsibirin Lombok na Kasar Indonesiya.

Cibiyar Bincike Kan Yanayin Kasa ta Amurka ta ce,  a kusa da garin Lombok na Indonesiya a yanki mai nisan kilomita 4 daga Belanting girgizar kasa mai akrfin awo 6.9 ta afkua karkashin kasa da zurfin kilomita 20.3.

Ba a bayar da sanarwar ko an samu asarar rai ko jikkata ba sakamakon girgizar.

A safiyar Lahadin nan ma wata girgizar mai karfin awo 6.3 ta afku a tsibirin na Lombok.

Makwanni 2 da suka gabata girgizar kasa mai karfin awo 7 ta afku a yankin inda sama da mutane 460 suka mutu.Labarai masu alaka