Isra’ila ta sake bude kofofin Masjidul Aqsa

A cewar shaidun gani da ido,a sayin safiyar yau,an sake bude masallacin Aqsa,wanda aka rufe a jiya,sakamakon afkuwar wani hari da makami.

Isra’ila ta sake bude kofofin Masjidul Aqsa

A cewar shaidun gani da ido,a sayin safiyar yau,an sake bude masallacin Aqsa,wanda aka rufe a jiya,sakamakon afkuwar wani hari da makami.

An dai rufe dukannin kofofin tsarkakken wurin ibadar da ke a gabashin Qudus bayan sallar La’asar,jim kadan bayan sojojin Isra’ila sun harbe har lahira wani matashin Bafalasdine,wanda suke ya yi yunkurin far musu dan wuka.

Falasdinawa sun yi sallar Magariba a gaf da sauran kofofin masallacin,wadanda suka hada Al-Asbat,yayin a lokacin sallar Isha kuma, sojojin azzalumar kasar Yahudu ta tarwatsa su.

Wannan shi ne karo na biyu da Isra’ila ke yi wa Musulmai karar kare tare rufe kofofin masallacin Aqsa.

Tag: aqsa

Labarai masu alaka