Wani jirgin sama dauke da mutane 9 ya yi layar zana a Japan

'Yan sandan Japan sun sanar da bacewar wani jirgin sama mai saukar ungulu samfurin Bell 412EP.

Wani jirgin sama dauke da mutane 9 ya yi layar zana a Japan

'Yan sandan Japan sun sanar da bacewar wani jirgin sama mai saukar ungulu samfurin Bell 412EP.

Sanarwar da aka fitar ta ce, an rasa sadarwa da jirgin.

Jirgin ya tashi da karfe 9:15 na safe daga garin Maebashi zuwa kan iyakar Gunma da nagano inda da misalin karfe 10.45 a lokacinda ake sa ran saukar sa aka neme shi aka rasa.

An iya samun sadarwa da jirgin mintuna 45 bayan tashinsa amma daga nan kuma ba a sake jin duriyarsa ba wanda yana dauke da ma'aikatan ceto 4 da 'yan kwana-kwana 5.Labarai masu alaka