Mutane 26 zaftarewar kasa ta kashe a Indiya

Sakamakon mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a jihar Kerala ta Kasar Indiya ambaliya da zaftarewar kasa sun afku inda ya zuwa yanzu mutane 26 suka rasa rayukansu.

Firaministan Kerala Pinyari Vijayan ya ce, za su gudanar da taron gaggawa game da ibtila'in da ya samu jihar.

A gefe guda kuma a garin Munnar ana ci gaba da kokarin kubutar da wasu 'yan yawon bude ido 30 da lamarin ya rutsa da su.

Hukumar Kula da Yanayi ta yi gargadin za a ci gaba da samun mamakon ruwan sama a yankin.Labarai masu alaka