Ɗan kunar baƙin wake ya kashe mutane huɗu a Afganistan

Wani harin ƙunar baƙin wake da aka kai a yankin Herat dake ƙasar Afganistan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu.

Ɗan kunar baƙin wake ya kashe mutane huɗu a Afganistan

Wani harin ƙunar baƙin wake da aka kai a yankin Herat dake ƙasar Afganistan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane huɗu.

Mai magana da yawun magajin garin Herat Jelani Ferhad ya bayyana cewar ɗan kunar baƙin waken ya tayar da bama baman dake jikinsa a cikin taro.

Baya ga wadanda suka rasa rayukansu wasu 12 sun raunana.

Mai magana da yawun asibitin Herat Muhammad Rafik Shirzoy ya bayyana cewar hudu daga cikin waɗanda suka raunana na cikin mayuwacin hali.

Kawo yanzu dai ba'a ɗora alhakin harin akan kowa ba.

 Labarai masu alaka