An ayyana dokar ta baci a Amurka

Sakamakon gobarar daji da ke ci gaba da ci ba kakkautawa a dajin Kasa na Clevaland da ke jihar California ta Amurka an ayyana dokar ta baci a jihar.

An ayyana dokar ta baci a Amurka

Sakamakon gobarar daji da ke ci gaba da ci ba kakkautawa a dajin Kasa na Clevaland da ke jihar California ta Amurka an ayyana dokar ta baci a jihar.

Jaridun California sun rawaito gwamnan jihar Jerry Brown na cewa, an ayyana dokar ta baci saboda yadda gobarar ta mamaye yanki mai girman kadada dubu 10,236. 

An kwashe dubunnan mutane daga yankin sakamakon gobarar.

Gobarar ta shafi jama'ar kauyukan Riverside da Orenge d ke yankin.

'Yan sanda sun ce, da gan-gan aka saka wutar wadda tuntsawon makwanni aka kasa shawo kanta.

Tag: Amurka , Gobara

Labarai masu alaka