"Duk dukiyar da Trump zai kashe ba zai iya sauya Qudus ba"

Shugaban lamurkan Siyasar Hamas lsmail Haniye, ya bayyana cewar tattakin da aka gudanar a zirrin Gaza domin kare martabar Falastin ya yi tasiri kwaran gaske.

A yayinda Haniye ke jawabi game da bukin ƙaramar salla ya bayyana cewar:

"Tattakin da Falasdinawa suka yi ya yi tasirin kare siyasa, tsaro da tattalin arzikin Falasɗinu"

Ya ƙara da cewa duk irin mataki da dukiyar da shugaba Trump zai kashe ba zai canja matsayar Qudus ba.

Ya kuma kara da cewa duk da irin kalubalen da muke fuskanta zamu ci gaba da haɗa kai domin kare martabar Falasɗin da kwarin gwiwa.Labarai masu alaka