'Yan ta'addar Houthi sun kai wa Saudiyya hari na 10 cikin watan Ramadhan

Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewar ta yi nasarar lalata makami mai linzami a yankin Jazan da kungiyar Houthi suka jefa mata.

'Yan ta'addar Houthi sun kai wa Saudiyya hari na 10 cikin watan Ramadhan

Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewar ta yi nasarar lalata makami mai linzami a yankin Jazan da kungiyar Houthi suka jefa mata. 

Gidan talabijin đin El-Ihbariyye na kasar Saudiyya ya rawaito cewa kungiyar Houthi dake Yaman suka harba makami mai linzami a kudancin Saudiyya 

A dayan barayin kuma gidan talebijin đin kungiyar Houthi El Misira ya bayyana cewar kungiyar Houthi ta harba makami mai linzami ne domin kalubalantar sojojin Al Faysal dake Jazan. 

Wannan ne dai karo na goma da Houthi suka harbawa Saudiyya makami mai linzami a cikin watan Ramadhan. 

Tag: Shi'a , Houthi , Hari , Yaman

Labarai masu alaka