An gano burbushin kura mai shekaru biliyan 4.5 a sararin samaniya

Masana a Amurka sun gano burbushin kura mai shekaru biliyan 4.5 a sararin Samaniya.

An gano burbushin kura mai shekaru biliyan 4.5 a sararin samaniya

Masana a Amurka sun gano burbushin kura mai shekaru biliyan 4.5 a sararin Samaniya.

Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka, NASA ta ce,tawagar masanan jami'ar Hawaii ta Amurka,wacce ke karkashin jagorancin masaniya Hope Ishii sun zurfafa bincike kan sassan wasu ababe da ta samo a kololuwar samaniyar duniyarmu, a dakin gwaje-gwajen na Berkeley da ke jihar California, ta hanyar amfani da tartsatsin wuta na musamman.

Sakamako ya nuna cewa,wadannan ababen na kunshe da burbushin kura mai shekaru biliyan 4.5.

Masanan sirrikan samaniya,sun tabbatar da cewa wannan kurar ta bayyana a lokaci daya da wasu tauraru masu wutsiya da suka biyo bayan halittar duniyar rana.

Ishii ta ce, kurar na da muhimmaci sosai musamman ma, wajen gano yadda tsarin rana,tauraru da kuma duwatsun samaniya suka kafu tun tashin farko.

Masanan sun wallafa sakamakon binciken a Mujallar "Proceedings of the National Academy of Sciences".Labarai masu alaka