Danmak: Aiki ko Azumi? Ku zabi daya !

Ministar shiga da fice ta Danmak ,Inger Stojberg,wadda ta yi kaurin suna haikan wajen kyamar masu neman mafaka, ta ce ko Musulman da ke aiki a kasarta su bar azumtar watan Ramalana,ko kuma su ajje aikinsu ga baki daya.

Stojberg ta ce ta dauki wannan matakin saboda,ma’aikata Musulmai masu yin azumi na iya jefa rayukan al’umar Danmak cikin babban hatsari.

Don raba zare da abawa game da ainahin abinda take nufi,ministar ta ce:

“Ba zai taba yiwu ba mu damka tsaro da kuma rayukanmu ga matukin motar da ya wuni da yunwa da kishin ruwa.   Wannan ai debo ruwan dafa kai ne, ko kuma in ce banka wa kai wuka.Shi yasa,aiki ko azumi ? su zabi daya ! Haka zalika wannan addinin (wato Islam) da aka kafa shi kan dokokin karnonin baya, ba ta da wani gurbi a rayuwarmu ta yau.Saboda yana cin karo da wayewarmu”.

 Labarai masu alaka