Saudiyya ta saka Sakatare Janar na Hizbullah Hassan Nasrullah a jerin sunayen 'yan ta'adda

Saudiyya ta saka sunan Sakatare Janar na Kungiyar Hizbullah da ke Labanan Hassan Nasrullah tare da mataimakinsa Naim Kasim da karin wasu mutane 8 a jerin sunayen 'yan ta'adda.

Saudiyya ta saka Sakatare Janar na Hizbullah Hassan Nasrullah a jerin sunayen 'yan ta'adda

Saudiyya ta saka sunan Sakatare Janar na Kungiyar Hizbullah da ke Labanan Hassan Nasrullah tare da mataimakinsa Naim Kasim da karin wasu mutane 8 a jerin sunayen 'yan ta'adda.

Rahotanni sun ce, Hukumomin na Saudiya sun kuma saka sunayen wasu kamfanunnuka 2 a jerin sunayen 'yan ta'addar.

Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya rawaito Sanarwar da Najalisar tsaron Kasa ta Saudiyya ta fitar wadda ta ce an saka Nasrullah da Kasim tare da kuma Muhammad Yezbek, Hussain Halil,Ibrahim Amin Al-Sayyid a jerin sunayen 'yan ta'adda.

Sanarwar ta ce, an dauki wannan mataki ne tare da hadin giwar Amurka, Bahrain, Kuwait, Oman, katar da Hadaddiyar Daular Larabawawadanda dukkan mambobin Kungiyar Yaki da Taimakawa Ta'addanci (TFTC) ne.

Sanarwar ta kuma ce, an kuma saka wasu masu taimakawa ta'addanci da suka hada da: Ali Yusuf Sharara, Hussain Ibrahim da Talal Hamiyye da kuma kamfanunnukan Spectrum Group daMahir Business Limited a jerin sunayen 'yan ta'addar.

Sanarar ta kara da cewa, duba da doka ta 1373 ta Majalisar Dinkin Duniya da ta hana taimaka wa ko daukar nauyin kungiyoyin ta'adda ne ya sanya aka saka mutanen da kamfanunnukan a jerin sunayen 'yan ta'adda kuma Saudiyya ta saka wa duk dukiyar da suke da ita a Kasar takunkumi.

A kwanakin baya ma Ma'aikatar Baitulmalin Amurkata saka Hassan Nasrullah, mataimakinsa Naim Kasim da wasu mutane 2 mambobin Hizbuşllah a jerin snayen 'yan ta'adda.Labarai masu alaka