Ramadan: Sakon Mahmud Abbas zuwa ga Falasdinawa

Shugaban kasar Falasdin Mahmud Abbas ya yiwa al'umar kasar fatan alhairi a cikin watan ramadana, a inda ya yi kira da su mutunta watan mai alfarma ta hanyar yin ibada.

Kanfanin dillancin labaren kasar Falasdinu WAFA ya rawaito cewar shugaba Abbas ya mika sakon azumi ga al'umar kasarsa.

A sakon na Azumi daga shugaba Abbas ya nemi al'umar kasasarsa da su kasance cikin bin dokokin addini a lokacin da suke murnar fara azumin.

Abbas ya nemi da a taimakawa wadanda ke cikin mawuyacin hali da kuma kira ga ma'aikatun kasar da su guji shirya bude bakin da ya wuce wuri.

 Labarai masu alaka