An yi zanga-zangar la'antar Amurka a Paris

A Paris Babban Birnin faransa na gudanar da zanga-zangar la'antar matakin da Amurka ta dauka na mayar da ofishin jakadancinta da ke Tel Aviv Babban Birnin Isra'ila zuwa Kudus.

paris israil protesto1.jpg

A Paris Babban Birnin faransa na gudanar da zanga-zangar la'antar matakin da Amurka ta dauka na mayar da ofishin jakadancinta da ke Tel Aviv Babban Birnin Isra'ila zuwa Kudus.

Kungiyoyi da ke neman goyon bayan Falasdinawa ne suka kira zanga-zangar inda mutum dubu suka taru a dandalin Trocadero da kusa da Hasumiyar Eyfel.

Mutanen sun la'anci hare-haren da Isra'ila ke kai wa Falasdinawa a Kudus.

A yayin zanga-zangar an bukaci Isra'İla da ta dakatar da kai harhare kuma Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanya wa Isra'ila takukumi.

Masu zanga-zangar sun dinga rera taken la'antar Amurka da Isra'İla inda suka aike da sakon goyon baya ga babban tattakin da Falasdinawa za su yi a Zirin gaza.Labarai masu alaka