"Muna iya yin kaca-kaca da Saudiyya cikin awanni 48 kacal"

Mashawarcin shugaban rundunar soja Iran,Janar Redha Kharam Tussi ya ce kamata yayi Saudiyya ta daina tsokanar su,saboda sun tanadi karfin da zasu iya ganin bayan ta cikin yawanni 48.

Tussi ya ce,

"Ina yi wa shugabannin Saudiyya hannunka mai sanda game da tsokanar fitina da kuma furta kalaman wuce gona da iri.Baku da karfi da kuma isassun makaman da zaku yi tinkaho da su.Awanni 48 kacal sun ishe mu yin kaca-kaca da kasarku.Shi yasa ku rufe bakunanku ku zauna"..

Game da tunkunmai da kuma cuzgunawar da Amurka ke ci gaba da yi wa kasarsa,Janaran ya ce,kasar Iran ta kasance a wani muhimmin matsayi,wanda ke sauwaka ma ta yin fito-na-fito da daya daga cikin manyan makiyanta, Amurka.

Janar Tussi dai ya furta wadannan kalaman don mayar wa da yarima mai jiran gado na masarautar Saudiyya,Muhammad bin Salman da martani dangane da cin fuskar da yi musu a ranar 29 ga watan Maris na bana tare da cewa nan da shekaru 10 zuwa 15 kasarsa za ta fafata yaki da Iran.

 Labarai masu alaka