NATO: Muna goyon bayan matakan Amurka akan gwamnatin Asad dari bisa dari

A taron kolin da kungiyar NATO ta gudanar a helkwatanta dake Brussels ta bayyana cewar tana goyon bayan matakin da Amurka, Faransa da Ingila suka dauka akan gwamnatin Asad dake kaiwa farar hula hari da makami mai guba.

Sakatare Janar na NATO Jens Stoltenberg, ya tabbatar da cewa hukumar ta bada gudunmowa akan harin da Amurka ta jagoranta a Siriya.

Stoltenberg a yayinda yake ganawa da manema labarai bayan taron kolin ya kara jaddada kyama akan amfani da makamai masu guba da gwamnatin Asad ke yi akan farar hula.

Stoltenberg, ya kara da cewa kafin gudanar da harin an bi duk ko wacce hanyar lumana ama lamarin ya faskara, a sabili da haka babu wata hanya da ta rage yanzu sai amfani da karfin soja.

A dayan barayin kuma a sakamakon taron da aka fitar an bayyana cewar kungiyar NATO ta goyi bayan harin da kasashen Amurka, Ingila da Farsansa suka kaiwa gwamnatin Asad dari bisa dari.

 Labarai masu alaka