Masu zanga-zanga sun fafata rikici da ‘yan sandan Faransa

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Faransa sun fafata rikici da ‘yan sandan kasar inda aka kama 51 daga cikinsu.

Masu zanga-zanga sun fafata rikici da ‘yan sandan Faransa

Masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Faransa sun fafata rikici da ‘yan sandan kasar inda aka kama 51 daga cikinsu.

Rundunar ‘yan sandan ta sanar da cewa, bayan gudanar da bincike an saki wasunsu inda aka tsare 17.

Kusan murane dubu 2 ne suka halarci zanga-zangar wadanda suka kuma kai hari kan bankuna, wuraren sana’a, ofisoshin inshora, shagunan sayar da waya da na dillalai da ke yankin.

Mahukunta sun ce, masu zanga-zangar sun janyo asara mai yawa a wuraren.

A lokacin da ma’aikata da dama ke yajin aiki a Faransa, wasu kungiyoyi kuma na zanga-zanga don neman wasu bukatu daga wajen gwamnati.

Dubunnan Faransawa ne suka fita kan tituna don neman bukatunsu.

‘Yan sanda sun yi amfani da karfi da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zangar.

 Labarai masu alaka