Likitoci sun tirsasa majinyaci yin matashin kai da yankakkiyar kafarsa

Shugabannin asibitin Uttar Pradesh na birnin New Delhi sun dakatar da wasu likitoci 2 wadanda suka tirsasa majiyacinsu yin matashin kai da yankakkiyar kafarsa, a yayin da suke yi masa tiyata.

An yanke shawarar daukan matakan da suka dace don hukunta wadanda suka aikata wannan laifin.

Majinyacin mai suna Ghanshyam,ya tsinci kansa hannun wadannan likitocin bayan wani kamazin hatari motar bus da ya yi.

Daya daga cikin makusantan Ghanshyam mai shekaru 28 da haihuwa, Janaki Prasad  ya fada wa manema labarai cewa isarsu asibiti ke da wuya, suka yi yunkurin sauya wa dan uwansu matashinkai amma likitocin suka kiya.

Asibitocin Indiya na a sahun gaba a jerin cibiyoyin kiwon lafiya marasa nagarta na duniya, kana suna fama da karancin kwararrun likitoci.

A shekarar bara ma, a asibitin Uttar Pradesh jinjirai da dama sun mutu sabili da rashin iskar oxygen, kana wani likitan bogi ya sa wa akalla muatane 46 kwakwayoyin cutar HIV.Labarai masu alaka