An ayyana 3 ga watan Afrilu a matsayin "Ranar Hukunta Musulmi"

A  "Ranar Hukunta Musulmi", za a bai wa duk wanda ya kai wa Makkah hare-haren bama-bamai maki 2,500,wanda ya kone masallaci maki 1000,wanda ya kashe Musulmi maki 500, wanda ya cire hijabin Musulma kuma maki 25.

Wasu da ba a san ko su waye ba, na ci gaba da aika wasiku masu kunshe wadannan garabasan ga al'umar Ingila, don ingiza su aikata hare-haren ta'adanci kan Musulmai da wururaren ibadarsu a ranar 3 watan Afrilun kowace shekara, wacce suka ayyana a matsayin "Punish a Muslim Day", wato "Ranar Hukunta Musulmi",inji kafafan yada labarai na Ingila.

Haka zalika,wasikun na gayyatar jama'ar kasar da su watsa wa Musulmai acid a fuska tare azabtar da su.

Wannan sabon lamarin ya razanar da Musulman Ingila matuka gaya,wadanda suke ci gaba da tambayar kan makomar 'ya 'yansu.

Tuni 'yan sanda suaka fara bincike don gano ainahin wadanda ke ci gaba da aika wadannan wasikun.

 Labarai masu alaka