• Bidiyo

Mummunar gobarar daji ta kashe mutane 9 a Indiya

Mutane 9 ne suka mutu sakamakon gobarar daji da ta kama a jihar Tamil Nadu ta kasar Indiya.

Mummunar gobarar daji ta kashe mutane 9 a Indiya

Mutane 9 ne suka mutu sakamakon gobarar daji da ta kama a jihar Tamil Nadu ta kasar Indiya.

Bayanan da kafafan yada labaran yankin suka fitar na cewa, gobarar ta kama a tsaunukan Kurangani da ke yankin Theni inda wasu mutane 9 da suke tattaki a dajin suka rasha rayukansu.

Rahotanni sun ce, wasu karin mutane 8 sun jikkata a lamarin.

An kai wadanda suka jikkata zuwa asibitocin yankin.

Ma'aikatar kashe gobara sun far wa wutar don kashe ta.

Tag: Gobara , Indiya

Labarai masu alaka