Shin ta yaya China ta zama dodanniyar Amurka ?

A gaban 'yan majalisar dattijan kasarsa,shugaban hukumar leken asiri ta Amurka,FBI,Christopher Wray ya bayyana dalla-dalla dalilan da suka haifar da fargabar China a zuciyoyinsu.

Shugaban na FBI ya ce :

"China na ci gaba da kokarin kwace matsayin farko na kasar da ta fi kowace karfi a duniya daga hannunmu, ta hanyar mamaye cibiyoyin ilimi da kimiyya da fasaha na kasar Amurka.Sin na da Farfesoshi,dalibai, da kuma masana masu dumbin yawa wadanda suka samu gindin zama a jami'o'inmu,manyan biranen kai har ma da kauyuka.Wadannan mutanen ba su da wani aiki,face aika milyoyin bayanai zuwa kasarsu.Ya kamata mu farga tun da wuri ko kuma China ta fi karfinmu"

Wani sanata na jam'iyyar Republican ma ya karfafa gwiwar Wray inda ya ce :"A tsawon shekaru 240 na tarihin kasarmu, bamu taba fuskantar wata kasa ta yi matukar razana mu kamar China ba"

Tag: fbi , sina , china

Labarai masu alaka