Trump ya aike da sakon ta'aziyya ga Putin

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump ya aike da sakon ta'aziyya ga takwaransa na Rasha Vladimir Putin bisa rasuwar mutane 71 a hatsarin jirgin sama a birnin Moscow a karshen makon da ya gabata.

Sanarwar da Fadar Shugaban Kasar Rasha ta fitar ta ce, shugabannin biyu sun yi musayar ra'ayi game da hatsarin.

Sanarwar ta kara da cewa, Trump ya mika wa Putin da jama'ar rasha baki daya gaisuwar ta'aziyyar ras mutanen 71.

Shugabannin sun kuma tattauna batun shawo kan rikicin Falasdin da Isra'ila.

Tag: Amurka , Trump , Putin

Labarai masu alaka