Idon wani mutum a Ingila ya makance saboda yawan Jima'i

Wani mutum a kasar Ingila ya rasa idonsa daya sakamakon yawan Jima'i kamar yadda wani rahoto da Likitocinsa suka bayar.

Idon wani mutum a Ingila ya makance saboda yawan Jima'i

Wani mutum a kasar Ingila ya rasa idonsa daya sakamakon yawan Jima'i kamar yadda wani rahoto da Likitocinsa suka bayar.

Mutumin da aka ki bayyana sunansa ya farka da safe tare da daina gani da idonsa wanda hakan ya sanya shi garzayawa zuwa asibiti tare da bayar da korafin abin da ya same shi farar daya.

A yayin gana wa da likitoci ya bayyana cewa, yana yawan yin jima'i. 

Sakamakon gwaje-gwajen da likitocin suka yi kuma ya nuna cewa, jijiyar idon mutumin ta tsinke a lokacin da ya yi wani godon numfashi yayinda kuma hanyar fitar da iska da ke makogwaronsa ta ke a rufe.

 Labarai masu alaka