An gano Koriya ta Arewa na yin wani surkulle mai hatsari a karkashin teku don hargitsa duniya

An gano cewa, Koriya ta Arewa na yin wani surkulle mai hatsari a karkashin kasa inda idan ta kammala za ta fara gwajin harba makaman Nukiliya daga karkashin tekun kasar.

Shafin yanar gizon na "38 North" ya fitar da bayanan gano aiyuka masu hatsari da Koriya ta Arewa ke yi wanda aka gano ta hanyar amfani da tauraron dan adam.

Daga cikin hotunan da aka nuna an ga yadda aka nutse kasan teku da wani jirgin ruwa dauke da makami mai linzami mai karfin gaske.

A wani nazari da babban jami'in cibiyar bincike kan Amurka-Koriya ta Jami'ar Johns Hopkins Mista Joseph S. Bermudez Jr an nuna hoton jirgin ruwa da gwammnatin koriya ta Arewa ta kai karkashin teku wanda ka iya harba makamin Nukiliya mai hatsari.

Hotunan sun kuma nuna wani abu da ake zaton na samar da iska ga mutane da ke karkashin teku tare da taimakawa wajen harba makaman.

Ganin kugiyar gini na motsi alamu ne da ke nuna cewa, ana ta aiki ba kakkautawa a karkashin tekun.

Koriya ta Arewa dai ta jima tana yi wa kasashen duniya barazana musamman ma a Amurka game da irin makaman Nukiliyar da ta ke gwada harbawa.Labarai masu alaka