Majalisar Dinkin Duniya: Saudiyya da kawayenta sun jefa al'umar Yaman cikin musiba

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da halin da jama'ar kasar Yaman suke ciki sakamakon yakin basasar da ake ci gaba da yi.

Mataimakin Sakatare Janar na Majalisar mai kula da Harkokin Dan Adam Mark Lowcok ya ce, ko dai a magance matsalar takunkumin da Saudiyya da Kawayenta suka saka a Yaman ko kuma a fuskanci matsalar bil'adama da ba a taba gani a duniya ba.

Lawcock ya yi jawabi bayan wani zaman sirri da Kwamitin tsaro na Majalisar ya gudanar inda ya ce, mutanen da cutar amai da gudawa ta kama a Yaman sun kai miliyan 1, inda mutane miliyan 21 kuma ke bukatar taimakon gaggawa.

Ingila da Faransa sun yi kira da a janye matakan hana kai kayan taimako Yaman.Labarai masu alaka