Tarayyar Turai: 'Yan ta'addar Daesh Turawa da dama sun koma kasashensu

Shugaban kwamitin Tarayyar Turai mai yaki da ta'addanci Gilles de Kerchove ya bayyana cewa, akwai Turawa da dama da suka yi yaki tare da Daesh a kasashen Siriya da Iraki da a yanzu suka koma kasashensu na Turai.

Tarayyar Turai: 'Yan ta'addar Daesh Turawa da dama sun koma kasashensu

Shugaban Kwamitin Tarayyar Turai mai yaki da ta'addanci Gilles de Kerchove ya bayyana cewa, akwai Turawa da dama da suka yi yaki tare da Daesh a kasashen Siriya da Iraki da a yanzu suka koma kasashensu na Turai.

Kerchove da ke ziyarar aiki a Tunisiya ya gana da ministocin tsaro da shari'a na kasar inda suka tattauna kan matakan da ya kamata a dauka na hadin gwiwa wajen yaki da ta'addanci.

Bayan ganawar tasu Kerchove ya zanta da 'yan jaridu inda ya ce, alkaluman Tarayyar Turai na nuna akwai Turawa da suka yi yaki da Daesh da dama a Siriya da Iraki wadanda suka koma kasashensu na Turai. 

Ya ce, sakamakon magance matsalar da za a iya fuskanta saboda dawowar 'yan ta'addar kasashensu to akwai bukatar Tarayyar Turai ta kare dukkan iyakokinta. 

Kerchove ya kuma kara da cewa, alakar Tarayyar Turai da Tunisiya na da karfi sosai kuma za su hada kai wajen yaki da fatauncin mutane da tsaurin ra'ayi.Labarai masu alaka