Mutane da suka mutu sakamakon gobarar daji a Amurka sun kai 41

Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 41 sakamakon gobarar daji da ta kama tun daren Lahadin da ta gabata kuma aka kasa shawo kanta a jihar Kalifoniya ta Amurka inda kuma har yanzu ba a da labarin wasu mutanen 174.

Gobarar ta kama a yankuna 17 daban-daban na Kalifoniya inda ma'aikatan kwana-kwana kusan dubu 11 tare da masu aikin sa kai suke kokarin kashe ta.

An kwashe kusan mutane dubu 100 a jihar ta Kalifoniya amma an ba mutane dubu 25 a wasu yankunan da aka kashe wutar izinin koma wa gidajensu.

Gidaje da wuraren sana'a dubu 5,700 ne suka kone a jihar.

Haka zalika wutar ta cinye yanki mai girman kilomita 898.Labarai masu alaka