Kotu a Amurka ta sake kunyata Trump

Kotun Tarayyar da ke Hawaii a Amurka ta dakatar da dokar da DOnald Trump ya saka na hana 'yan wasu kasashen duniya 8 shiga kasar wadda ta fara aiki a ranar 24 ga watan Satumba.

Mai Shari'a Derrick Watson ne ya yanke hukuncin bisa dalilin nuna wariya ga 'yan wasu kasashen waje.

Fadar White House kuma ta ce, wannan hukunci na Watson babban kuskure ne mai hatsari.

Sanarwar da Fadar ta fitar ta ce, an umarci ma'aikatar Shari'a da ta dauki matakin da ya kamata nan da nan.Labarai masu alaka