Mutane 5 sun mutu sakamakon mamakon ruwan sama a China

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayyana cewa, mutane 5 ne suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a jihar Hubey ta kasar China.

Sakamakon ambaliyar an kuma kwashe mutane dubu 26,700 daga matsugunansu, an rushe gidaje dubu 8,500 yayinda gonaki masu girman Hekta dubu 253 suka samu matsala.

An bayyana cewa, asarar da aka yi ta kai ta dala miliyan 608 inda mahukunta suka ce an aike da jami'an ceto zuwa yankin.

A watan da ya gabata ma mutane 5 sun mutu inda aka kwashe wasu dubu 27 daga gidajensu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Sha'ansi da ke China.Labarai masu alaka