TRT World za ta shirya Babban Taro inda za a tattauna matsalolin duniya

A ranar 18 ga watan Oktoba birnin Istanbul zai karbi bakuncin wakilai daga kasashen duniya daban-daban inda za a tattauna kan matsalolin da ke damun duniya baki daya.

TRT World za ta shirya Babban Taro inda za a tattauna matsalolin duniya

A ranar 18 ga watan Oktoba birnin Istanbul zai karbi bakuncin wakilai daga kasashen duniya daban-daban inda za a tattauna kan matsalolin da ke damun duniya baki daya.

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ne zai yi jawabin bude taron wanda tashar Talabijin ta TRT World za ta shirya. 

Wannan ne karo na farko da TRT World za ta gudanar da wannan babban taron wanda za a tattauna matsalolin siyasa, al'adu, tattalin arziki da zamantakewa inda wakilai daga kasashen duniya da dama da suka hada da 'yan siyasa, 'yan kasuwa, masu fafutuka, malaman jami'o'i da 'yan jaridu za su halarta.

Taken babban taron shi ne "Samar da sauyi a zamani na rashin tabbas".

Daga cikin wadanda za su yi jawabi a wajen akwai tsohin firaministan Spaniya Jose Luis Rodriguez Zapatero da ya sha fama da batun kuri'ar raba gardama, 'yar Malcom X mai fafutuka Ilyasah Shabaz, Ministan harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Çavuşoğlu, Ministan Cigaban Kasa na Afirka ta Kudu Olive Dlamini, Darakta Janar na TRT Ibrahim Eren da kuma Darakta Janar na RUSI Karin von Hippel.

Haka zalika akwai Musulma Minista ta farko a Ingila Barones Sayeede Warsi wadda ta yi murabus saboda irin manufofin da kasarta ta ke nuna wa game da Gaza.

A wajen taron da za a tattauna batutuwan siyasa da nauyin da ke kan kafafan yada labarai, za kuma a tattauna batutun nuna kyamar Musulunci, taimaka wa dan adam, da kuma hanyoyin da kasashen duniya za su bi wajen magance rikice-rikicen da ake fuskanta.

A yammacin 18 ga watan Oktoba za a gudanar da wannan babban taron inda za a yi bayani game da shirin "TRT World Citizen" da kuma yadda TRT World ke ci gaba da kara bayar da hima wajen warware rikicin da ake fuskanta a duniya da irin rawa da ta ke taka wa.

Kanun wannan shiri shi ne yaran 'yan gudun hijira da suka bata.

Za kuma a gudanar da shirye-shiryen gaskiya kan yadda lamarin 'yan gudun hijira ya ke.

Shugaban Sashen labarai na TRT World Fatih Er ya bayyana cewa, suna gudanar da wani shiri na gaskiya game da yadda yara kanana suke fada wa hannun bata gari.

Domin samun bayanai game da taron za ku iya ziyartar adireshin yanar gizo kamar haka: forum.trtworld.comLabarai masu alaka