Dakarun Turkiyya na ci gaba da aiyukan bincike a Siriya

Dakarun sojin Turkiyya na ci gaba da gudanar da bincike tare da sanya idanu kan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka amince da ita a Siriya inda suke kuma neman guraren da za a kafa sansanonin kula da yankunan zaman lafiyar kasar da za a kafa.

Dakarun Turkiyya wani bangare ne na rundunonin kasashe 3 da suka sana hannu kan yarjejeniyar kafa yankunan zaman lafiya a Siriya inda a ranar 8 ga watan Oktoba suka fara aiyukan bincike da sanya idanu a yankin Idlib.

Dakarun Turkiyya za su dinga sanya idanu a cikin Idlib inda na Rasha kuma daga wajen lardin.

Manufar wanzuwar sojin Turkiyya a Siriya shi ne a tabbatar da aiki da tsagaita wuta, dakatar da arangama, samun damar mika kayan taimako ga jama'a, mayar da wadanda suka bar gidajensu zuwa garuruwansu da kuma nemo hanyar kawo karshen rikicin kasar baki daya.Labarai masu alaka