Mutane 7 sun mutu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu a Indiya

Mutane 7 ne suka mutu sakamakon hatsarin wani jirgin sama mai saukar ungulu mallakar sojin Indiya wanda ya fado a arewa maso-gabashin kasar.

Sanarwar da rundunar 'yan sanda ta fitar ta ce, jirgin mallakar sojojin saman kasar ne kuma ya fado a yankin Tawang mai tsaunuka wanda ke a jihar Arunachal Pradesh.

An bayyana ana ci gaba da binciken musabbabin hatsarin.

A 'yan watannin nan ana yawan samun fadowar jirage masu saukar ungulu a Indiyainda gwamnatin kasar ke cewa, kuskuren mutane da matsalar inji ce ke haddasa hadurran.Labarai masu alaka