An kashe mutane da dama a wani hari da aka kai kan wani Hubbare a Pakistan

Mutane 20 ne suka mutu yayinda wasu 25 suka samu raunuka sakamakon harin bam da aka kai a kofar shiga wani hubbare da ke jihar Balujistan ta kasar Pakistan.

Mahukunta sun ce, jami'an tsaro ne suka tare maharin a lokacin da ya yi kokarin shiga hubbaren inda nan da nan ya tayar da bam din da ke jikinsa.

A gefe guda kuma Turkiyya ta la'anci harin da aka kai inda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fiyar da sanar cewa, tana matukar bakin c,iki game da harin da aka kai a jihar Balujistan ta Pakistan inda mutane da dama suka mutu tare da jikatar wasu.Labarai masu alaka