An zartarwa da wata mata hukuncin kisa a Amirka

Bayan shekaru 70, a karon farko an yankewa wata mata hukuncin kisa a jihar Georgia ta Amirka.

An zartarwa da wata mata hukuncin kisa a Amirka

Tun a shekarar 1997 ne matar ta kashe mijinta, kuma kotu ta yanke mata hukunci, amma sai a daren ranar Larabar nan aka kashe ta ta hanyar yi mata allurar guba.

Matar mai suna Gissendaner ta hada kai da saurayinta, inda ta cakawa mijinta wuka kuma ya ce ga garinku nan.

Sakamakon rashin samun gubar da aka yanke hukuncin a yi mata allura ne ya sanya aka dage zartar da hukuncin a watan Maris.

Lauyoyin Gissendaner sun bukaci da a janye hukuncin kisan a ranar Talatar da ta gabata, inda kotun ta ce za ta yi nazari game da hakan.

Amma kotun daukaka kara ta Amirka ta yi watsi da wannan bukata, tare da kin karbar bukatar kwamitin afuwa na jihar Georgia.Tag:

Labarai masu alaka