Tarihin TRT

TRT – Milestones
1 ga watan Mayu 1964 kamar yadda labarin yazo cikin 359 sakamakon tsarin mulkin kasar Turkiya an kafa cikakken kamfanin gidan rediyo da talabijin kuma ya samu cikakkiyar damar gudanar da tashoshin rediyo na jaha.
31 ga watan Janairu 1968.
TRT gidan talabijin na Ankara ya fara gwajin farko
9 ga watan Satumba 1974
Gidan rediyon na Turkiya ya fara aiki awa 24 a karkashin sunan TRT1
17 ga watan Afrilu 1979
TRT ta shiya ranar yara na kasa da kasa ranar 23 ga watan Afrilu inda aka kawo taron kai tsaye a tashoshin turai 27.
6 ga watan octoba 1986
TRT-2 ta fara aiki
2 ga watan Octoba 1989
Tashoshin gidajen talabijin na TRT-3 DA TRT-GAP da aka fara lokaci daya
28 ga watan Fabrairu 1990
Tashar TRT International da TRT-INT sun fara aiki a nahiyar turai
30 ga watan Yui 1990
Tashar ilii TRT-4 ta fara aiki daga Izmir
3 ga watan Disamba 1990 TRT ta fara gwaji da teletext da sunan Telegun
27 ga watan Afrilu 1992 tashar TRT Eurasia ta fara watsa labarai ga jama’ar jamhuriyar Turkiya a matsayin masu sauraro na farko.
14 ga watan Nuwamba 1998 aka bude ofishin TRT na Berlin.
5 ga watan Janairu 1999 ne aka bude cibiyar watsa labarai da na’ura mai kimiya (SAYTEEK)
1 ga watan Mayu 1999 aka kaddamar da shafin yanar gizo na TRT.
15 ga watan Yuli 1999 labaran TRT-FM da na Voice of Turkey ya kai Autralia.
25 ga watan Yuli 1999 ne shirye shiryen TRT-INT TV ya kai Australia da kuma New Zealand.
20 ga watan Satumba 1999
An bude ofishin TRT Ashgabat a Turkmenistan .
6 ga watan satumba 1999
Radio-4 ya fara watsa labarai
7 ga watan Yuni 2000
TRT-INT da Voice of Turkey (TSR) da TRT-FM(Radio-2) shirye shiryensu ya kai Amurka da Canada.
31 ga watan Janairu 2001
Tashoshiin TRT-TV sun canza ainihin hukomi da kuma sabon tambari
2 ga watan Yuna bude ofishin i TRT Baku.
16 ga watan Yuni 2001 aka bude ofishin TRT Alkhahira .
1 da watan Yuni 2002 ne TRT ta kawo cikakken wasannin gasar cin kofin duniya na 2002 wanda South Korea da Japan suka dauka nauyi Seouland a kasar Tokyo inda kungiyar kwallaon kafa ta Turkiya tayi na uku a gasar.
25 ga watan Yuni 2002 aka bude ofishin TRT na biyar a Brussels
2 ga watan Yuni 2002
TRT Tourism Radio ya fara aiki awa 24.inda ya bude wuri a Lara da kuma ya bude tasha Antalya inda ya fara kai wad a sauraro a cikin harshen Turanci,Faransanci,Jamusanci,Rashanci da Greek
8 ga watan Agusta 2002 TRT ta bude ofishin tan a shida a kasar waje a garin Washington DC
24 ga watan Mayu 2003 Turkiya ta lashe gasar EuroVision na 48 da wakar Way that I can wadda Sertab Erener yayi.
20 ga watan Janairu 2004 TRT TA kaddamar da shirye shiryen tan a zamani a tashoshin :TRT-1,TRT-2,TRT-3,TRT-4 da TRT-INT TV da kuma duka TRT Radio a tauraron Turksat 1C.
12 ga watan Mayu 2004 TRT ta dauki nauyin wakar kasar Eurovision a garin Istanbul.A gasar da aka gudanar ta farko a matakai biyu na farko inda aka watsa shirin kai tsaye ga kasashe 36.
3 ga watan Nuwamba 2004 ne aka canza shafukan yanar gizo na TRT zuwa www.trt.net.tr kuma aka kara canza fasalin.A ciki harda tsarin da aka canza don saukin aiki don kawo sauki ga bincike akan yanar gizo.aka canza mazallin don kawo sauki sannan shafin yanar gizo ya kara sauri baki daya.Talabiji da Rediyo da kuma shirye shiryen prime-time da aka fara don baki masu ziyarar shafin su samu don samun cikakken bayanai game da shirye shirye baki daya.
14 ga watan Disamba 2004 aka kaddamar TRT-Turk Tv da kuma TSR-Turkish a gaba na tauraron Turksat 1C wanda ya kunshi kasar Turkiya gaba daya da Asia ta tsakiya.
24 ga watan Yuni 2005 TTRT ta bude ofishinta a bakwai a garin Tashkent
10 ga watan Agusta 2005 samu nasarar fara watsa shirye shirye na Olympics na kasa da kasa na Universiade Izmir kai tsaye a shekra ta 2005.
1 ga watan Nuwamba 2005 TRT-Asia-Pacific Broadcasting UUnion (ABU) aka sanya hannu akan yarjejeniyar na Asia Vision.
22 ga watan Yuni 2006 bayan yarjejeniya da gidan talabijin na Buena Bista.TRT ta siya yancin ikon watsa labarai na shekara 4 zuwa Walt Disney Co,Majigin yara,rayarwa da fina fina a Turkiya.
16 ga watan Maris 2007 ne TRT ta sayi lasisin watsa gasar cin kofin duniya harda kamar su wasannin FIFA, gasar cin kofin Confederation daga lokacin 2010 zuwa 2014.
13 zuwa 20 ga watan Afrilu 2008 TRT ta samu lasisin watsa gasar kekuna na kasa da kasa wanda shugaban kasa ya shirya da akayi Turkiya.