Rediyon TRT

REDIYON TRT

TASHOSHIN REDIYON TRT

Koyaushe mukan yi korafi game da cigaban kimiyya da fasashar kere-kere kasancewar irin wannan cigaban ya zo lasarmu a makare. Wannan batu ya sabawa matsayin zuwan rediyo. Na'urar rediyo ta zo Turkiyya kusan lokaci daya da sauran kasashen duniya a ranar 6 ga watan Mayun shekarar 1927. An kuma kafa sabon tarihi a lokacin da aka kafa gidan rediyo da telebijin na  Turkiyya (TRT) a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 1964.

A yanzu haka kafafan watsa labaran TRT sun kurade dukkan sassan kasar Turkiyya da kuma dukkan bangarorin al'umma unda ake watsa shirye-shiryen don jama'a ta hanyar amfani da ka'idodji da manufofin watsa shirye-shirye, yayinda shirye-shiryen suka hada da labarai, ilimi, al'adu, wakoki da kuma nishadi.

Yada shirye-shiryen rediyo ta kafafen TRT na da matukar tasiri a kasarmu da ma duniya. Rediyoyinmu su ne ka ar haka; Radio-1, Radio-2 (TRT FM), Radio-3, Radio-4, Reddiyoyin shiyya guda biya dake garuruwan ( Antalya, Çukurova, GAP-Diyarbakir, Erzurum, Trabzon), TRT  Folk Song (wakokin gargajiya) ga masu sha'awar irin wadannan wakokin, TRT news (labarai) da kuma rediyinmu na kasa da kasa wato muryar Turkiyya wanda ke yada shirye-shirye cikin harsuna 32, sannnan sai Europe FM.

 

TRT Radio 1

Wannan tasha ta farko ta mayar da hankali wajen shirya shirye-shiyen ilmantarwa, labarai da al'adu. Tana biyan bukatun duk wani mai son samun labarai ko ilimi. Tana watsa shirye-shiryenta a dukkanin fadin Turkiyya ta hanyar yanar gizo, satellite da transmitters. Shirye-shiryen tsahar da suke ba wa kowa hakkinsa da nuna son kai sun shafi bangarorin kimiyya, adabi, wasanin kwaikwayo, wasannin zamani, muhalli, tattalin arziki da kuma labarai.

 

TRT Radio1

Tun daga shekarar 1927 zuwa yau ko'ina da akwai rediyo a Turkiyya.

 

Radio-2 (TRT FM) 

Wakoki da nishadantarwa, ta karade dukkan fadin Turkiyya da ma duniya baki daya ta hanyar setillite da yanar gizo. Wannan abokiyar tafiyarmu ce zuwa ko'ina domin ta na zuwa kaso 99,9 cikin dari na zangonta.

 

TRT FM

Tashar rediyo ce da ta yanke duk wani nisa.

 

 

Radio-3 

Wannan tasah tana bayar da zababbun wakoki da kade-kade inda tafi mayar da hankali ga wakokin Elvis Presley zuwa Joan Baez, Frank Sinatra zuwa Thaikowsky sai kuma Mozart zuwa Sara Vaughan, inda ta hada da sabbi da tsaffin wakoki. Watsa shiryen-shirye ta studio inda ta karade Turkiyya gaba daya da kuma duniya ta hanyar setillite da yanar gizo.

 

 

TRT 3

Na kawo ingantattun wakoki da kade-kade

 

Radio-4

Dukkanin wasu nau'o'in kade-kaden gargajiya suna wannan tsashar....kidan Saz semai-kade-kaden Turkiyya na gargajiya da ake yi algaita, ko garaya, wadanda wani bangare ne na wakokin kasar. Wakokin gargajiya, wakokin soyayya, wakokin tuna baya da duk sauran nau'in wakoki na soyayya da kuma wakokin gargajiya na yankin Anatoliya na kwararrun makada algaita tun daga zamanin da har zuwa yanzu....duk akwai su a wannan tashar. Tana watsa shirye-shirye kullum da dukkanin fadin Turkiya da ma duniya ta hanyar setillite da yanar gizo.

 

TRT Radio 4

Ita ce magaryar tukewa wajen bukata

 

 

TRT kade-kaden gargajiya wadda ta fara yada shirye-shirye a ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2009, tasha ce wadda take biyan bukatun masu son wakokin gargajiya ta hanyar amfani da akwatin radiyoyinsu, yanar gizo da kuma setillite. Manufar tashar shi ne kara saka larsashi ga masu sauraronta don son kad-kaden gargajiya na Turkiyya. Ta hada da tsantsar kidan gargajiya wanda kuka gada kaka da kakanni, kuma tana ba da gudunmowa don adana al'adu da yada su.

 

 

TRT Nağme, wannan tashar ta fara yada shirye-shiryenta tun shekarar 2009. TRT Nağme na biyan bukatun masoya kade-kaden gargajiya ta FM, setillite da kuma yanar gizo. TRT Nağme na gabatar da shirye-shiryenta cikin awanni 24, inda ake kawo kade-kade daga taskar wakokin Turkiyya, tare kuma da sabbi. Wakoki da ake yi yanzu.

 

 

TRT Radio News (TRT Labarai)

 Wadannan tashoshi ne na shiyya a Antalya, Çukurova, GAP-Diyarbakir, Erzurum da Trabzon. Suna watsa shirye-shiryensu daga karfe 10:00 zuwa 13:00 na kowacce rana. Suna ba da labarai game da duk al'amuran da suka shafi yankunan. 'Anadolu Kuşağı' na watsa shirye-shiryenta da karfe 13:00 a TRT Turku. Kowacce tashar shiyya na watsa shirye-shirye zuwa kowanne lungi da sako ja Turkiyya.

 

 

Muryar Turkiyya, na watsa shirye-shiryenta daga Ankara a kan gajeren zango. Ana iya sauraron muryra. Turkiyya a fadin duniya tun sama da shekaru 70 da suka wuce. Tana yada labarai, wasanni, al'adu, adabi da kuma kade-kade don nishadantarwa. Muryar Turkiyya wata gada ce da take hada Turkiyya da 'yankasarta da suke kasashen waje, da kuma kasashen dake da alaka da kasar wajen yare, da kuma al'adun Turkiyya, tsashr kuma na taimakon mutanen idan suna cikin halin bukata tare da yada manufofinsu. Tana watsa shirye-shirye na tsawon awanni 24 ta gajeren zango, setillite, da kuma yanar gizo. Za ka iya sauraron muryar Turkiyya a ko'ina kake a fadin duniyar nan.

 

 

Tashar TRT ta Kurdawa na yada shirye-shirye don kawo hadin kan kasa inda an samar da ita ga dukkan al'uma. Ta fara watsa shiri a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2009. Raediyon ta 6 na isa ga kudu maso gabashin yankin Anatoliya. Tana lara dankon zumunci tsakanin gwamnati da mutanen yankin, tana kuma yin tasiri mai kyau wajen alaka da kasashen duniya.

 

 

'TRT Europe FM' tasha ce dake a yankin Anatoliya; tana sanar da yadda yanayin rayuwa take da jindadinta, yadda ake gudun hijira, yada al'adun Turkiyya, bukatar Trukawa da kuma kade-kadensu. Nan tattaunawa a tashar tare da matasa da suka zama matasan. Tashar na yada shirye-shiryenta kullum daga karfe 09:00-18:00 agogon Turkiyya, haka kuma akwai ta a yanar gizo da kuma setillite. Idan kana so ka saurari wakar da ka fi so, za ka nemi a saka maka.