Game da TRT

TRT-Takaitaccen Tarihi

Hukumar gudan Rediyo da Telebijin ta Turkiyya.

An kafa TRT wadda ita kadai ce kafar yada labarai ta gwamnati ta farko a Turkiyya, a ranar 1 ga watan. Mayun shekarar 1964.

Gidan radiyon da ya fara watsa shirye-shirye a ranar 5 ga watan Mayun 1927 yanzu yana karkashin i uwar TRT. Radiyon kan sadu da mu daga ko'ina a fadin duniya da zarar mun kamo ta, kuma a karshen shekarar 1960 ta samu abokiya wato telebijin....Turkiyya ta kafa tata telebijin din a ranar 31 ga watan Janairun 1968.

Kasancewar bangaren rediyo na da shekaru 81, telebijin kuma na da 40, TRT ta kasance abar tunawa a tarihin Turkiyya, bisa aiyuka da dawainiyarta, aba ce da za a amince da ita kuma alama ce ta hadin kanmu.

Rayuwar yarintaka tabbas ta kan zo da matsalali da kalubale. An fara aiki a dakin watsa shirye-shirye dake Mithatpasha a cikin yanayi mara kyau. Amma sakamakon karsashin ma'aikatan da sadaukarwarsu na magance kalubalen, suka zage dantse da kokari suka canja al'amarin cikin kankanin lokaci, wanda hakan ya sa TRT ta samu matsayi na musamman a zukatan Turkawa. A zamanance kuma, kasancewar tashar ta watsa labarai kuma ita ce aka fi dogaro da ita a Turkiyya kuma tare da ma'aikatanta kwararrundake samun nasara. A saboda haka shirye-shirye masu kyau da kayatarwa na zuwa daka TRT.

TRT ba wai kawai tashar watsa shirye-shirye ba ce ta rediyo da telebijin, ta zama makaranta ce ta bayar da ilimi. Kuma wannan ilmantarwar ba wai ta tsaya ga ma'aikatanta ne kawai ba har ma ta hanyar watsa shirye-shirye da labaranta tna ilamantarwa.

TRT ta zama zakaran gwajin dafi a duniya tsakanin sauran tashoshi saboda abubuwa na ma'ana da take gabatarwa masu inganci da kaye.

Za mu iya lasafta abubuwan da suka tabbatar da wannan nasara kamar haka:
We can possibly outline the factors bringing about this success as follows:

Watsa shirye-shirye masu inganci kuma abin dogaro

Wasu da aka tattauna da su a birnin Washington na Amurka, Brussels na Belgium, Alkahira na Masar, Berlin na Jamus, Nicosia na Cyprus bangaren Turkiyya, Baku na Azerbaijan, Ashgabat na Turkmenistan, Tashkent an Uzbekistan da ma sauran lunguna na duniya........ A takaice dai TRT ta kafu a ko'ina tun daga Turai, Amurka, Asiya, gabas ta tsakiya da ma Caucasia.

Akwai 'yanjaridu da kowa ya kware a bangarensa da aka samar a shiyyoyin TRT da suka hada da Istanbul, Izmir, Antalya, Çukurova, Diyarbakir, Erzurum, da kuma Trabzon bayan babbar hedkwatarta dake birnin Ankara; kuma ga aiki ga jama'a yadda ya kamata a ko'ina.

Alamun amincewa da gasgatawa daga masu kallonta da sauraronta, sabod dogaro da gaskiyar shirye-shiryen labaranta.

Watsa shirye-shirye ga kowanne bangare na al'uma

Ilimi, al'adu, kade-kade-nishadantarwa, shirye-shiryen yara da na wasanni, husuma, shirye-shiryen adana bayanai, wasan kwaikwayo, kawo fina-finan da suka fi kowadanne....isa ga jama'a da dama a matakan ilimi, shekaru, zamantakewa da tattalin arziki daban-daban ta hanyar shirye-shiryenta da suka dace da duniya da zamani kuma ake iya kallo da sauraronta daga ko'ina a fadin duniya. Tana da tashoshin telebijin 7, tashoshi 4 na cikin gida inda 2 na kasa da kasa da kuma 1 ta shiyya.


Tashashin telebijin

TRT 1: tashar iyali, awa 168

TRT 2: tashar labarai, sanarwa, al'adu da adabi, awa 168

TRT 3: tashar matasa da wasanni, awa 54

TRT GAP: tana watsa shirye-shirye ga shiyyoyin gabas da na kudu maso gabashin Turkiyya, awa 69.


TRT 4: tashar ilmantarwa da kade-kade, awa 139


TRT INT: tana watsa shirye-shirye ga duniya baki daya, awa 168

TRT TURK: wannan tashar na watsa shirye-shirye ga yankunan gabas ta tsakiya da caucasia, tana daukar awanni 119

TRT wata babbar gada ce da take hada 'yanjaridun nahiyar Turai, Asiya da na caucasia ta hanyar amfani da na'urar setillete ta kasa da kasa da kuma tashoshi guda 2 dake kasa; kasancewar tana iya yada irin cigaban da kasar Turkiyya le samu da kuma kudirorin duniya ta hanyar ba da cikakkane bayani nan take ta hannun hukumomin watsa labarai na kasa da kasa da take da alakar aiki tare da su.


A tashar TRT-TURK, tashar na kara rungumar 'yanuwanmu dake Caucasus da gabas ta tsakiya wajen yada labarai, da nuna al'umar Turkiyya ga duniya, da kuma yada harshe da samar da hadin kai tsakanin kasashe masu magana da Turkanci ta hanyar nuna goyon baya, taimakawa cigaban al'adu da hrkokin lasuwanci.

Ba da gudunmowa wajen habaka alakar al'adu tsakanin Turkiyya da Turkawa dake kasashen waje ta kafar TRT-INT wanda ake watsa shirye-shiryenta musamman don mutanen dake zaune a nahiyar Turai,mkuma ake iya kallonta a sauran sassan duniya.

Ta hanyar karfafa TRT-INT, daga matsayinta ta yadda za ta yi gogayya ga sabbin hukumomi da kamfanonin dillancin labarai masu zuwa na kasa da kasa.

Tashoshin telebejin na TRT da ake aikin gina su yanzu

Hidimtawa 'yankasa dake magana da yaruka daban-daban a yankuna daban-daban amma wadanda suke da kamanceceniya ta fuskar harshe. Kokarin da ake na a samar da sabuwar tasha a yarukan Kirmachi da Zaza.....akwai manufar watsa shiri a yaren Farisa da Larabci don kara kulla dangantaka tsakanin wadannan yarukan.

Ana kuma kokarin kafa sabuwar tasha domin yara, wadda za rika watsa shirye-shirye a Turkiyya da ma duniya baki daya.

Shekaru 81 na aikin rediyo

Tashashin rediyo na TRT har yanzu su ne manyan abokan jama'a a Turkiyya, tana da tashoshi 4 na cikin gida, biyar na shiyya da kuma karin wata tashar ta yawon dube ido. Tana da kwararrun ma'aikata, tana amo a dukkan bangarorin kade-kadeda wakoki, mawaka kwararru, kungiyoyin yara da dalibai, ma'adani mai cike da bayanai, watsa shirye-shirye ta na'ura mai kwakwalawa, dakunan watsa shirye-shirye da aka samar musu da kayan aiki na zamani.

Tashoshin rediyo

Radio 1: ilmantarwa, al'adu da tashar watsa labarai. Tana da matukar muhimmanci ga masu sauraronta tsawon shekaru 8 na aiyukanta da suka shafi dukkan batutuwan labarai a kowacce sa a.

Radio 2: (TRT FM): tashar watsa kade-kaden da suka yi fice, misali wakkokin zamani na Turkiyya, na gargajiya, da kuma pop.

Radio 3: wakoki da kade-kaden zamani na Jazz da Opera

Radio 4: kidan gargajiya na Turkiyya da kuma na zamani

Duk wadannan tashoshi na cikin gid kuma suna watsa shirye-shirye tsawon awanni 24 a fadin Turkiyya gaba daya, da kuma duniya ta yanar gizo.

Tashoshi biyar na shiyya
Radiyoyin Trabzon, Erzurum, GAP-Diyarbakir, Antalya, Cakurova,... tashar yawon bude ido ka na taka muhimmiyar rawa wajen hidimtawa Turkawa 'yan yawon bude ido da ma baki.

Tashar Global Radio Broadcast na yada shirye-shirye a yaruka 29

Muryar Turkiyya na sadarwa tsakanin Turkawa dake rayuwa a kasashen waje da kuma kasarsu ta gado cikin yarika 29 da suka hada da Turkanci, inda kuma take isar da kasar ga dukkan sassan duniya.

Watsa shirye-shirye ga duniya baki daya

Tashar watsa shirye-shirye da take da manufofi masu gudana, wadda cikin hanzari ta tattara dukkan wasu kayan fasaha na watsa labarai, ta hanyar kwarewar da take da shi.

Wannan abubuwan da ta tattara a harkar watsa shirye-shirye ya ja hankalin kasar wajen cigaba da samun nasara saboda kayayyakin aiki da take da su. Muna yada shirye-shirye a ciki da wajen kasarmu inda muke da tashoshin telebijn 66 dake da karfin megawatt 61 da kuma wasu rediyo dake da karfin megawatt 22 wadda duk tafi sauran kafafan yada labarai masu zaman kansu a Turkiyya.

Akwai setillite guda biyu wadanda suke iasar da shirye-shiryenmu na rediyo da telebijin ta setellite din TURKSAT 2A da TURKSAT 1C (3A). Bayan haka, TRT tasha ce dake dA dakunan yon shirye-shirye guda 42 wanda daya daga ciki yana birnin Berlin na kasar Jamus.

Tashoshin tafi da gidanka 9 dake watsa shirye-shiryenmu ta telebijin

Akwai tashashoin telebijin ma setillite dake yada shiri kai tsaye a Turlmenistan da diyarbakir.

A radio satellite up-link interview caravan,

Akwai rediyo ta setillite dake tattaunawa da mutane.
Akwai shirye-shiryen rediyo 55 da ake yi a dakunan yada shirye-shirye.
Akwai setillite guda 9 da aka kafa na telebijin da rediyo
Da kuma rediyo guda biyar dake watsa shiri kai tsaye.
Da kuma motoci shida dake daukar injin ba da hasken lantarki.

Ana yin shirye-shiryen gwaji na tsawon awanni 24 a Ankara, Istanbul da Izmir.
Trial programs are aired 24 hours non-stop in Ankara, Istanbul and Izmir.

TRT a yanar gizo
A kokarin da take na biyan bukatun jama'arta a wannan zamani na cigaban fasaha, TRT ta kawo shirye-shirye msu kyau cikin kankanin lokaci. Adresinta na yanar gizo shi ne http://www.tr.net.tr wand aka kaddamar a ranar 1 ga watan mayun shekarar 1999. Akwai kuma shirye-shirye kai tsaye a yanar gizo don biyan bukatun jama'ar duniya su amfana da TRT, ta fuskar cigaban tattalin arziki da cikayya da hada-hadar kudi, wasanni, hasashen yanayi, da kuma sauran shirye-shiryen radiyo da telebijin.