'Yan Najeriya na koyon zayyana da taimakon Turkiyya

Malam Yusha’u Abdullah da ya koyi Zayyana da Zanen Ayoyin Alkur’ani Mai Tsarki na bayar da horo kan wannan sana’a a garin Kaduna dake arewacin Najeriya.

'Yan Najeriya na koyon zayyana da taimakon Turkiyya

Malam Yusha’u Abdullah da ya koyi Zayyana da Zanen Ayoyin Alkur’ani Mai Tsarki na bayar da horo kan wannan sana’a a garin Kaduna dake arewacin Najeriya.

Horon da ake bayarwa a cibiyar IRCICA irin ta ta farko a Afirka ta Yamma na ci gaba da aiyukan6a tare da taimakon Turkiyya.

Dalibai a cibiyar na koyon zane da kayan aikin da aka kawo daga Turkiyya.

Masu koyon zanen na fuskantar matsaloli saboda yadda a kasarsu babu kayan zanen da ake bukata, amma Cibiyar Bincike da Raya Al’adu da Sana’o’in Musulunci (IRCICA) tare da taimakon Turkiyya na samar musu da wadannan kayan aiki.

Daya daga cikin masu zane a cibiyar Shiyya ta IRCICA Idris Umar ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, suna horar da masu sha’awar koyon zane ta hanyar taimakon da suke samu daga Turkiyya.

Umar ya ce, su daliban Malam Yusha’u Abdullah ne, kuma ya koya wa ‘yan Najeriya da dama wannan sana’a ta zane.

Umar ya ja hankali kan yadda gwamnatin Najeriya da kungiyoyi masu zmaan kansu ba sa bayar da gudunmowarsu wajen koyon zanen inda ya ce “ıdan za a fada karara gaskiya ba a san muhimmancin wannan zane a nan ba shi ya sa ake fuskantar matsaloli.”

Umar ya ce “Tun shekarar 2011 ya fara nuna sha’awar koyon zanen. Tun ina yaro karami na ke son koyon wannan sana'a.”

“Ina ji na kamar a Ina yawo a wata duniya”

Umar ya bayyana godiyarsu bisa taimakon da Turkiyya ba su, kuma idan dalibansu suka kammala koyon zanen za su je Turkiyya don karbar shaidar kwarewa a zanen.

Ya ce “Idan ina zane ina jin farin ciki. Sai na ji kamar ina yawo a wata duniyar.”

“Sanin muhimmancinsa ne ya sanya muke yi”

Daya daga cikin daliban cibiyar Amina Jaafar ta fadi cewa, “Tsawon shekaru 2 na yi ina samun horo kan zanen kuma ba don kudi na ke yin hakan ba. Kuma ma ai ba za ka yi zanen don ka samu kudi a Afirka ba. Amma saboda yadda muke mayar da hankali da sha’awar abun ya sanya muke yi.”

Amina ta godewa Turkiyya bisa irin taimakon da ta ke ba wa wannan cibiya tasu.Labarai masu alaka