An gano wani kwaro a Masar da aka busar da gangar jikinsa

A garin Giza na Masar a yayin hakar kayan tarihi an tono busasshen gangar jikin wani kwaro mai kama da mulmula kashi (Scarabaeus sacer) wanda a imanin jama'ar Helipolitan shi ne ubangijin rana Khepri.

misir giza kazi1.jpg
misir giza kazi2.jpg
misir giza kazi3.jpg
An gano busassun wasu kwari da aka yi imani da aiyukansu a tarihin Masar
An gano busassun wasu kwari da aka yi imani da aiyukansu a tarihin Masar

An gano busassun wasu kwari da aka yi imani da aiyukansu a tarihin Masar

A garin Giza na Masar a yayin hakar kayan tarihi an tono busasshen gangar jikin wani kwaro mai kama da mulmula kashi (Scarabaeus sacer) wanda a imanin jama'ar Helipolitan shi ne ubangijin rana Khepri.

A yayin taron manema labarai don shaidawa duniya an gano kwaron na Scarabaeus sacer, Ministan Ma'aikatar Adana Kayan Tarihi ta Masar Khalid Al-Anani da Sakataren Hukumar Mustafa Waziri da Jakadun kasashen Waje ne suka halarta.

A yayin taron Waziri ya ce, gano wannan kwaro ya zama wani babban abu ga Masar da duniya baki daya.

Waziri ya kuma ce, da suka tambayi sauran gidajen ajje kayan tarihi ko suna da irin wannan abu sai suka ce, su kawai akwatuna ne ba wai wanda aka busar ko kandararwa ba.

Waziri ya ci gaba da cewa, a ranar 10 ga Afrilu aka fara aiyukan hakar inda suka samu wani akwati mai dauke da Scarabaeus sacer guda 200 da aka busar da su, tare da wata busasshiyar mage da busasshen maciji. Haka zalika sun gano wani littafin Fir'auna da aka bayar da tarihinsa.

Ministan Ma'aikatar Adana Kayan Tarihin ta Masar Anani kuma cewa ya yi, a wannan yankin dai sun gano wani zaki daka daskarar da shi tare da wasu maguna da kuma kaburburan Fir'aunoni 7.Labarai masu alaka