An kai hari kan wata babbar makabartar Musulmai a Jamus

A jihar Lower Saxonya dake kasar Jamus wasu masu kyamar Addinin Musulunci sun kai hari kan Makabartar Muslmai dake garin Northeim.

An kai hari kan wata babbar makabartar Musulmai a Jamus

A jihar Lower Saxonya dake kasar Jamus wasu masu kyamar Addinin Musulunci sun kai hari kan Makabartar Muslmai dake garin Northeim.

A yayin harin an rubuta alamar Kuros da jan fenti a jikin Kaburbura 12 da kuma katangarta.

An kai harin a daren Asabar din da ta gabata inda aka yi rubutun nuna kyamar Musulunci a jikin wasu duwatsu dake wannan makwanci.

Wasu maziyarta Makabartar a ranar Lahadin da ta gabata ne suka ga an kai harin inda suka kuma sanar da 'yan sanda wanda suka bayyana an samu asarar dukiya a harin.

'Yan sanda sun bukaci hadin kai da goyon bayan jama'ar yanki a binciken da suka fara gudanarwa inda suka ce ma duk wanda ya ga me ya faru ya je ya bayar da shaida.Labarai masu alaka