Ya koyi sana'ar zane a Turkiyya, yana koyarwa a Najeriya da Yammacin Afirka baki daya

Malam Yusha'u Abdullah ya koyi sana'ar zane a Turkiyya tsawon shekaru 5, a yanzu yana koyar da wannan sana'a ga matasan Najeriya maza da mata dake sha'awar koya tare da samun sana'ar dogaro da kai.

Ya koyi sana'ar zane a Turkiyya, yana koyarwa a Najeriya da Yammacin Afirka baki daya

Malam Yusha'u Abdullah ya koyi sana'ar zane a Turkiyya tsawon shekaru 5, a yanzu yana koyar da wannan sana'a ga matasan Najeriya maza da mata dake sha'awar koya tare da samun sana'ar dogaro da kai. Ya kuma yi wa Masallatai da dama ado a Najeriya

Malam Abdullah mai shekaru 50 ya bude wajen koyar da koyon zane da rubutun Arabiyya a garin Kadunan arewacin Najeriya mai suna "Al-Mihrab  Calligraphy Center" inda yake koyar da dalibai matasa maza da mata wanda hakan ke bayar da dama wajen yaduwar wannan ilimi da sana'a a Yammacin Afirka baki daya.

Abdullah ya fara koyon wannan zane da kansa shekaru 29 da suka gabata, saboda bai samun inda zai koya a kasarsa ta Najeriya ba sai ya shiga neman tafiya Turkiyya ko Iran don koyon wannan zane mai kyau. 

Masanin zane Abdullah ya ce "Saboda ban san wani kwararre kan wannan zane a Yammacin Afirka ba sai na fara koya kuma jama'a suna nuna sha'awar abubuwanda na rubuta. Amma na kasance ina da burin habaka wannan sana'a tawa hakan ya sanya na fara tunanin tafiyar Turkiyya ko Iran don koya sosai."

Ya bude makaranta saboda bukatar yada zanen a Afirka

Masanin rubutu da zanen Arabiyya Abdullah ya bayyana cewar, a shekarar 2007 ya shiga jami'ar Mimar Sinan inda ya koyi rubutu da zanen daga wajen Hasan Celebi, Davut Bektas da wasunsu.

Ya ci gaba da cewa "Ana kallon 'yan Afirka a matsayin malalata ko marasa kwazo wajen koyon zane. Saboda haka ne na halarci makarantar Sakandire ta Kimiyya tare da kammalawa da kyakkyawan sakamako. Kuma sabo Ina sha'awar koyon zane ban damu da sai na karbi tallafin karatu daga jam'o'i da dama a Najeriya ba."

Abdullah ya ce, ya yi kokari sosai tare da jurewa wajen koyon wannan zane da rubutu mai kayatarwa, kuma bayan ya koma kasarsa Najeriya a shekarar 2012 sai ya bude makarantar bayar da horo don yada ilimin a Afirka.

Kwararren masanin ya ce "A Kaduna na ke a rayuwa kuma na bude makarantar koyar da zane a garin. Akwai dalibai da yawa dake daukar darasi a wajena. A yanzu ina da dalibai 25."

Yana nuna wannan sana'a a kasashe da dama

Malam Abdullah ya je kasashen duniya da suka hada da Turkiyya, Najeriya, Pakistan da malaysia don nunawa duniya irin aiyukan da ya gabatar na zanen Arabiyya.

Ya ce, sakamakon gudunmowa da goyon bayan Cibiyar arihin Musulunci, Sana'ar Hannu da Raya Al'adu ta (IRCICA) za a kafa cibiyar koyar da wannan zane ta farko a Najeriya Yammacin Afirka gaba daya.

Ya ce, ya yi wa Masallatai da dama ado da wannan rubutu a garuruwa da dama da suka hada da Kano, Abuja, Kaduna, Fatakwal.

Ya kuma ce a lokacin da yake koyon wanna sana'a a Turkiyya bai taba jin cewra shi bako ba ne saboda jama'ar kasar na da so da kauna baki dake zuwar musu.

Kwararren Masanin Zanen Arabiyya (Calligraphy) Malam Yusha'u Abdullah ya ce, "Turkiyya na daya daga cikin manyan kasashe masu muhimmanci, kuma idan mutum na son koyon wannan sana'a to babu kamar Turkiyya saboda sun taimaka min sosai."

TRT HaberLabarai masu alaka