Matsayin Ziyarar Erdogan a yankin Gagauz da alakar Turkiyya da Maldova

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci kasar Maldova inda ya je kuma yankin Gagauz mai zaman kansa inda Turkawan Gagauz suke rayuwa.

Matsayin Ziyarar Erdogan a yankin Gagauz da alakar Turkiyya da Maldova

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci kasar Maldova inda ya je kuma yankin Gagauz mai zaman kansa inda Turkawan Gagauz suke rayuwa. A wannan makon za mu kalli wannan ziyara ta Erdogan da irin tasirin da ta ke da ita kan maufofin Turkiyya a kasashen waje. Kamar kowanne mako za mu gabatar muku da sharihin Dr Jamil Dogac Ipek dake sashen nazazarin alakar kasa da aksa a jami’ar Karatekin da ke nan Turkiyya.

A kwanakin da suka gabata yankin Gagau Mai Cin Gashin Kansa dake Maldova ya karbi bakncin wata ziyara mai muhimmanci. Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ziyarci Maldova wanda a cikin shekaru 19 shi ne shugaban Turkiyya na farko da ya je kasar. A rana ta 2 ta ziyarar Erdogan ya je yankin Gagauz mai zaman kansa wanda ke a kasar ta Maldova. A ranar 18 ga Oktoba shugaba Erdogan ya zitarci Kumrat Babba Birnin yankin Gagau tare da Shugaban Kasar Maldova Igır Dodon.Shugabar yankin na Gagauz Mai Zaman kansa Irina Vlah ta tarbi Shugaba Erdogan bayan saukar su a ajirgi mai saukar ungulu inda jama’a dauke da tutar Turkiyya dake tsimayinsa suka jeru tara da yi masa maraba. Shugaba Erdogan ya wuce zuwa ginin Majalisar Zartarwa kamar yadda aka tsara inda suka gudanar da taro tare da Dodon da Vlah.

Shugaba Erdogan ya jagoranci bude aiyukan cigaban tattalin arziki da zamantakewa. Ya aike da sakonni dake nuna muhimmancin da yankn yake da shi ga Turkiyya a bangaren siyasa da tattalin arziki inda ya nuna cewar duk da yanki ne na tsohuwar tarayyar Sobiyet amma yana da muhimmanci kwarai da kara karfi ga Turkiyya.

A cikin ziyarar ta Erdogan ya kaddamar da sabon asibitin yara da Turkiyya ta gina a Komrat Babban Birnin Yankin Gagauz, wajen rainon yara kanana, Cibiyar Raya Al’adu da aka yi wa kwaskwarima, sannan a Lunga ya bude gidan ajje gajiyayyu. Shugaba Erdogan a jawabin nasa a Komrat ya tabbatar da za a tafiyar da matsalar ruwan sha dake damun al’umar yankin Vulkanesht. Ya sanar da a shekara mai zuwa za a fara gina babbar cibiyar ilimi a Komrat. Sannan wata sanarwa da ya kara bayarwa mai muhimmanci ita ta Turkiyya za ta bude ofishin jaakdancinta a Komrat.

Shugaba Erdogan ya bayar da sakonni na musamman ga Turkawan Gagau Kiristoci da suka jima suna jiran sa. Waannan sakonni sun ja hankali sosai. Shugaba Eerdogan ya gargadi jama’ar gagauz da su tsaya su koya tare da amfani sosai da yaren Kasar Maldova da suke cikinta, sannan kuma su ba wa yarensu na asali muhimmanci. Amma wannan gargadi da kira abin takaici babu yaren na Turkanci da jama’ar gagauz suke magana da shi. Yankin ya zama wani yanki da babu Turkanci a cikinsa duk da irin taimakon cigaban tattalina rzikin da Turkiyya ke wa yankin.

Yankin Gagauz na da yaruka a hukumance. Yaren Turkancin gagauz da aka amince da shi a a 1995, Yaren Maldova da na Rasha. A yankinnan gagauz da Turkawa suke kaso 82 cikin dari yaren Rasha ne a kan gaba. Musamman ma a manyan garuruwa za a iya ganin hakan karara inda wasu na kokarin koyon yarensu na asali. Amma masu matsakaitan shekaru da matasa ba su iya yarensu na sal, ba ko kadan, wasu kuma sun dan iya. Turkanci Gagauz ana yin sa kawai a wakoki, tatsuniyoyi, da kuma manyan mutane ma’ana tsofaffi dake magana da shi sai kuma wasu kafafan yada labarai dake samun tallafi daga Turkiyya.

Turkiyya ta amince da Maldova a matsayin kasa mai cin gashin kanta a watan Disamban shekarar 1991 bayan maldovan ta sanar da samun ‘yan cin kai a wannan shekarar. A ranar 3 ga watan Fabrairun shekarar 1992 kasashen biyu suka kulla alakar diolpmasiyya. A lokacin ziyarar shugaban kasar Turkiya na 9 Sulaiman Demirel zuwa Maldova a tsakanin 2 da 3 ga watan Yunin 1994 kasashen biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar “Kawance da Hadin Kai”. A ranar 1 ga watan Nuwamban 2012 aka sanya hannu kan yarjejeniyar janyrewar ‘yan kasashen biyu visa.

A ‘yan kwanakin nan da suka gabata, yarjejeniyar ta sake samun armashi sosai. İnda manyan shugabannin kasashen biyu sulka ziyarci juna.  Ziyarar Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ma na da ma’ana sosaia a wannan batu. Alkaluman shekarar 2016 sun nuna kayan da Turkiyya ke fitarwa zuwa Maldova a shekara sun kai na dala miliyan 189 inda maldova kuma ke kai na dala miliyan 313 zuwa Turkiyyan. A ranar 1 ga watan Nuwamban 2016 Turkiyya da Maldova sun sanya hannu kan yarjejeniyar saukakawa juna a bangaren kasuwanci.

Turkiyya ce kasa daya tilo dake bayar da taimako ga yankin Gagauz ba tare da jiran ta amfana da wani abu daga yankin ba. Wannan abu ne da kowa ya san, a wannan yankin. İrin Taimakon da Hukumar TIKA ta bayar a wannan yanki yana da yawa sosai. TIKA ta warware matsalar ruwan sha dake damun jama’ar Gagau. Kara larfafa gidan redyo da talabijinna Gagauz, kafa dakin karatu na Ataturk, taimakawa jami’ar Kumrat da gina gidan ajje tsofaffi, gyara ginin majalisar dokoki, yin kwaskwarima ga asibiti, gna makarantu da wajen rainon yara kanana na daga cikin daruruwan aiyukan taimako don cigaba da Turkiyya ta yi a yankin Gagauz mai zaman kansa ta hannun Hukumar TIKA. A lokacinda Turkiyya ke yin wadannan aiyuka ba ta tsoma bak a harkokin cikin gida na Gagauz ko Maldova. Akasin haka ma kokari take wajen ganin zaman lafiya ya dauwama a yankin.

 A jawabin da Shugaba Erdogan ya yi a Komrat ya bayyana cewar yankin kasar Maldova gaba daya na da matukar muhimmanci ga turkiyya da jama’arta. Kuma dole ne a koyaushe mu kalli kasar baki daya. Turkiyya ba ta son ta yi amfani da yankin Gagauz wajen yakar rasha da Yammacin duniya kan karfin ikon da suke da shi a Maldova. Kadda akr gani shi ne Turkiyya na tunanin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin Maldova da Gagauz. Sakamakon haka Shugaba Erdogan ya yi ta nanata cewar yankinna Gagauz ya yi zamansa a karkashin Maldova. Wannan batu na da muhimmanci. Wannan abu na sake hana jama’ar gagauz manta yarensu, haka kuma naaikewa da sako ga Rasha kan masu goyon bayan hadewar Maldova da Romaniya.   

A karshe, wannan ziyara ta Erdogan ta nuna yadda shugaban ya yi tsayin daka wajen kare martabar Turkawa Kiristoci dake tsakanin tsaka mai wuyar Yammacin Duniya da Rasha. A saboda haka za mu iya cewar taimakon da Turkiyya ke ba wa yankin Gagauz zai ci gaba da habaka a shekaru masu zuwa.

 Labarai masu alaka