Yau ake bukukuwan cika shekaru 95 da kafa Jamhuriyar Turkiyya

A ranar 29 ga watan Oktoba ne al'umar Turkiyya suke gudanar da bukukuwan murnar zagayowar Ranar Jamhuriya da aka ayyana shekaru 95 da suka gabata.

Yau ake bukukuwan cika shekaru 95 da kafa Jamhuriyar Turkiyya

A ranar 29 ga watan mtoba ne al'umar Turkiyya suke gudanar da bukukuwan murnar zagayowar Ranar Jamhuriya da aka ayyana shekaru 95 da suka gabata.

Bayan kammala yakin kwatar 'yancin kai da na duniya na farko a lokacinda aka rusa Daular Usmaniyya, Turkiyya karkashin jagorancin Mustafa Kamal Ataturk ta ayyana kanta a matsayin Jamhuriya.

An ayyana Jamhuriyar a ranar 29 ga watan Oktoban shekarar 1923 wato shekaru 95 kenan da suka gabata.

Sakamakon wannan rana Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya fitar da sanarwa inda ya bayyana cewar "Babu wata matsala, babu wani kalubale babu kuma wata kutingwilar da zata iya hana mu cimma burinmu"

Erdoğan ya kara da cewa, mun daura damarar sanya Turkiyya daya daga cikin kasashen duniya wadanda suka habbaka tare da inganata tattalin arzikinmu da siyasarmu. Ya kara da cewa: Katabaren filin tashi da saukar jiragen saman Istanbul da muka gina babbar alamace akan yunkurin gina kasarmu da muke yi.Labarai masu alaka