An ayyana zaman makoki na kwana guda a Iran

Sakamakon harin ta'addanci da aka kai a yankin Ahvaz na Iran gwamnatin kasar ta sanar da zaman makoki a ranar Litinin din nan.

An ayyana zaman makoki na kwana guda a Iran

Sakamakon harin ta'addanci da aka kai a yankin Ahvaz na Iran gwamnatin kasar ta sanar da zaman makoki a ranar Litinin din nan.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce, sakamakon harin ta'ddaanci da aka kai a garin Ahvaz majalisar ministoci ta bayar da ranar Litinin a matsayin ranar makoki ta kasa.

Sanarwar ta ce, za a binne wadanda aka kashe a harin a wajen bikin da za a yi a Tehran inda aka kuma mika sakon taaziyya ga iyalansu 

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka kai hari a garin Ahvaz da Larabawa suka fi yawa a lokacinda ake taron sojoji na tunawa da shekaru 28 da yakin Irak. An kashe mutane 25 da suka hada da sojoji 17 tare da jikkata wasu 60 a harin.Labarai masu alaka