Mawakiyar La Casa de Papel ta iso Turkiyya

Hamshakiyar mawakiya Cecilia Krull, wacce ta rera wakar shirin fim din "La Casa de Papel"mai farin jini a duk fadin duniya, ta kawo ziyara birnin Santambul.

Mawakiyar La Casa de Papel ta iso Turkiyya

Hamshakiyar mawakiya Cecilia Krull, wacce ta rera wakar shirin fim din "La Casa de Papel"mai farin jini a duk fadin duniya, ta kawo ziyara birnin Santambul.

Cecelia wacce ta fito daga wani gidan mawakan kasar Spain,kana ta fara kidan Jazza yayin da ta ke da shekaru 7 da haifuwa, ta hadu da masoyanta a zauren IKSV.

A gaban dubban ma'abotanta wadanda suka halarci shagalin da ta shirya,Krull  ta rera wakar "My Life is Going On", kidan taushin fim din "La Casa de Papel" wanda Manel Santisteban ya rubuta da kuma wasu wakoki biyu wadanda ta tsakuro daga wani kundin wakokinta.

Cecelia Krull wacce ta shahara haikan wajen rera wakoki a yaruka daban-daban na duniya,za ta kara ganawa da masoyanta na Santambul a zauren IKSV.Labarai masu alaka