Ambaliyar ruwa ta afku a Indiya

Mutane sama da dubu 650 sun tagayyara sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Odisha ta Indiya.

Ambaliyar ruwa ta afku a Indiya

Mutane sama da dubu 650 sun tagayyara sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a jihar Odisha ta Indiya.

Labaran da jaridun yankin suka samu daga hukumar bayar da agaji na cewa, kusan kauyuka dubu sun kasance a karkashin ruwa inda aka kwashe mutane dubu 15 daga matsugunansu zuwa wurare masu tsaro.

A wannan shekarar sama da mutane 400 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da hsadurra da ruwan sama a ya janyo a Indiya.Labarai masu alaka