Gimbiyar kasar Japan ta kawo ziyara Turkiyya

Gimbiyar kasar Japan Akiko Mikasa ta kawo ziyara a Turkiyya domin sada zumunci ga al'umar kasar.

Gimbiyar kasar Japan ta kawo ziyara Turkiyya

Gimbiyar kasar Japan Akiko Mikasa ta kawo ziyara a Turkiyya domin sada zumunci ga al'umar kasar.

Ta dai samu tarbo daga shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan a Mabeyn Köşkü dake birnin Istanbul.

Ba'a dai bari manema labarai sun halarci tarbon ba.

Gimbiya Akiko Mikasa za ta kasance a Turkiyya har ranar 14 ga watan Satumba.

Za ta kai ziyara a gururuwan Istanbul, Ankara da Kırşehir domin ganawa da al'umar biranen.

 Labarai masu alaka